Rikici ya haɗiɗiye Zaben fidda Gwani na jihohin Neja, Taraba, Imo da Bauchi

Rikici ya haɗiɗiye Zaben fidda Gwani na jihohin Neja, Taraba, Imo da Bauchi

Mun samu rahoton cewa rikici mai tsanani ya mamaye zaben fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC a wasu jihohi hudu dake fadin kasar nan ta Najeriya inda ya yi sanadiyar jikkatar kimanin mutane 17 tare da salwantar ran mutum guda.

Rahoton kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, jihohin da rikici ya haɗiɗiye zaben fidda gwanayen takarar na jam'iyyar APC sun hadar da Imo, Neja, Taraba, da kuma Bauchi.

Lamarin a can jihar Neja ya auku ne a yayin da aka yi arangama tsakanin magoya bayan wasu manema takarar kujerar majalisar wakilai biyu na jam'iyyar da yayi sanadiyar gadarwa da kimanin mutane 15 munanan raunuka.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, rikicin ya kuma yi sanadiyar yiwa wasu motoci 10 lahani mallakin daya daga cikin manema takarar kujerar ta majalisar wakilai, inda 'yan bangar siyasa suka yi amfani da makamai kama daga adda zuwa zabira wajen yiwa junan su lahani.

Rikici ya haɗiɗiye Zaben fidda Gwani na jihohin Neja, Taraba, Imo da Bauchi
Rikici ya haɗiɗiye Zaben fidda Gwani na jihohin Neja, Taraba, Imo da Bauchi
Asali: Twitter

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari da cewar rikicin ya auku ne a sanadiyar artabu tsakanin tsakanin magoya bayan wasu manema takarar kujerar majalisa biyu a jam'iyyar APC.

Majiyar rahoton ta kuma bayyana cewa, Matasa a mazabar Sarkin Dawaki dake karamar hukumar Jalingo can jihar Taraba, sun kai hari tare da yiwa wata mota mummunan lahani mallaki wani jigo na jam'iyyar APC, Ahmad Yusuf.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaban hafsin sojin sama ya je mika ta'aziyya ga Mahaifan Sojan Saman nan da Ajali ya katsewa hanzari

Can jihar Imo kuma fusattatun matasa sun tayar da tarzoma cikin kananan hukumomin Ohaji/Egbema, Oguta da kuma Mbaitoli, inda suka cinna wuta kan wasu motoci domin bayyana rashin goyon bayan su ga Uche Nwosu, dan takarar da gwamnan jihar Rochas Okorocha ke goyon baya.

Kazalika lamarin ya yi tsanani a jihar Bauchi inda rai guda ya salwanta baya ga tsananin jikkata ta wasu mutane biyu yayin da rikici ya kicime ana tsaka da gudanar da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan na jam'iyyar ta APC.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel