Jihohi guda 6 da jam’iyyar APC ta dage zaben fitar da yan takarar gwamna a cikinsu

Jihohi guda 6 da jam’iyyar APC ta dage zaben fitar da yan takarar gwamna a cikinsu

Uwar jam’iyyar APC ta fasa gudanar da zaben fitar da yan takarkarun mukamin gwamnoni a jihohin Najeriya guda shidda, inda ta dage gudanar da zabukan zuwa wani lokaci na daban, kamar yadda gidan rediyon muryar Amurka ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban jam’iyyar APC, reshen Arewacin Najeriya, Sanata Lawal Shuaibu ne ya sanar da haka da yammacin ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba, inda ya tabbatar da wannan matakin da uwar jam’iyyar ta dauka.

KU KARANTA: Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamnan APC a Adamawa ya kafa hujja

Jihohin da wannan mataki ya shafa sun hada ne da jahar Bauchi, Zamfara, Ogun, Legas, Abia da Jahar Imo, yayin da aka gudanar da zabukan fitar da gwanin a sauran jihohi talatin, manya daga cikinsu akwai jahar Kano, Kaduna, Katsina, Adamawa da dai sauransu.

Da dama daga cikin johin shidannan sun fuskanci dage zabe ne sakamakon rikita rikitan siyasa daya dabaibaye cikin gidar jam’iyyar APC, kamar a jahar Legas inda ake samun takun saka tsakanin jagiran APC Bola Tinubu da Gwamna Ambode.

Haka zalika jahar Imo ana samun tirka tirka tsakanin gwmanan jahar Rochas Okorocha wanda ya rantse sai ya daura surukinsa, kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, da kuma mataimakinsa Eze Madumere wanda akan burinsa na tsayawa takarar gwamna aka tsigeshi daga mukaminsa.

Zaben fitar da gwani da aka yi a jahar Yobe ya fitar da sakataren jam’iyyar APC ta kasa, Mai Mala Buni a matsayin wanda ya lashe wannan zabe, yayin da jam’iyyar PDP ta fitar da Umar Damagum a matsayin dan takararta na gwamnan jahar Yobe.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kano Abdullahi Gandue ya samu sama da kuri’u miliyan biyu da dubu dari bakwai a zaben fitar da gwani da aka yi shi kato bayan kato a Kano, haka zalika takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufai ya sami sama da kuriu dubu biyu a zaben fitar da dan takara da wakilan jam’iyar APC suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel