Abinda Buhari ya fada bayan karbar takardar murabus din Mama Taraba

Abinda Buhari ya fada bayan karbar takardar murabus din Mama Taraba

A jiya ne ministar mata ta kasa, Aisha Jummai Alhassan, ta ajiye mukaminta tare da ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki da kuma shiga jam'iyyar UDP inda ta yanki katin shaidar zama mamba da sayen fam din takarar gwamna.

A yau ne bayan dawowar shugaba Buhari daga kasar Amurka inda ya halarci taron a majalisar dinkin duniya ya karbi takardar murabus din da tsohuwar ministar ta rubuta.

A takarda da shugaba Buhari ya saka wa hannu da kansa, shugaban kasar ya ce, "Na karbi takardar murabus dinki daga mukamin ministar mata ta Najeriya. Na amince da murabus dinki ba tare da bata lokaci ba.

"A madadi na da gwamnati da jama'ar Najeriya, muna yi maki godiya da irin gudunmawar da ki ka bayar ga kasa.

Tuni shugaba Buhari ya umarci Hajiya Aisha Abubakar, karamar ministar raya masana'antu da saka hannun jari, ta saka ido a harkokin ma'aikatar mata.

Abinda Buhari ya fada bayan karbar takardar murabus din Mama Taraba
Mama Taraba
Asali: Twitter

A jiya, Asabar, ne tsohuwar ministar harkokin mata, Sanata Aisha Jumma Alhassan, ta sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar United Democratic Party (UDP).

Sanata Jummai wacce akafi sani da Mama Taraba ta yi murabus daga kujeran minister da shugaba Buhari ya nada ta saboda hanata takarar kujeran gwamnan jihar Taraba da jam’iyyar APC tayi.

A sakatariya jam’iyyar UDP, Jummai Alhassan ta bayyana cewa ta fita daga jam’iyyar APC ne saboda rashin adalci da akayi mata.

DUBA WANNAN: Zaben cikin gida: Sakamakon zaben Buhari daga jihohi 5

A ranar Juma'a ne Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce jam'iyyar ta dakatar da ministan watsa labarai, Adebayo Shittu tare da takwararsa ta ma'aikatar harkokin mata, Aisha Al-Hassan daga tsayawa takara karkashin jam'iyyar don kare martabobin da jam'iyyar ta shimfida.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

A cewar sa, tuni dokokin Nigeria suka warware komai dangane da batun yin NYSC. Dangane da ministar harkokin mata kuwa, Aosha Al-Hassan, ya ce an cireta ne saboda jam'iyyar bata gamsu da biyayyarta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel