Da dumi-dumi: Gwamna Shettima ya zabi wanda ya ke son ya maye gurbinsa

Da dumi-dumi: Gwamna Shettima ya zabi wanda ya ke son ya maye gurbinsa

- Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya zabi Farfesa Babagana Zulum a matsayin wanda ya ke son ya maye gurbinsa

- Gwamnan ya yi wannan sanarwan ne a wata taron da ya yi da masu neman takarar gwamna 21 da ke jihar

- Sai dai gwamnan ya ce zabinsa ba ya nufin sauran 'yan takarar ba su da damar fitowa a fafata da su a zaben fidda gwani

Gwamna mai barin gado na jihar Borno, Kashim Shettima ya zabi Farfesa Babagana Zulum a matsayin wanda ya ke son ya maye gurbinsa a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne sa'o'i kadan kafin a gudanar da zaben fidda gwani na 'yan takarar gwamna a jihar.

Da dumi-dumi: Gwamna Shettima ya zabi magajinsa
Da dumi-dumi: Gwamna Shettima ya zabi magajinsa
Asali: Getty Images

Mr Zulum, wanda shine tsohon Kwamishina ta hukumar Kulawa da wadanda rikicin ta'addanci ya shafe su yana daya daga cikin 'yan takara 21 da ke neman tikitin takarar gwamna a jihar ta Borno.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Gwamnan ya bayar da sanarwan ne a daren jiya Asabar yayin da ya ke jawabi ga masu neman takarar tikitin gwamna a jihar.

Duk da cewa manema labarai basu samu shiga inda ake taron ba, wata majiya daga taron ta ce gwamnan ya ce bayyana zabinsa cikin 'yan takarar bai zai hana sauran masu sha'warar takarar su shiga a fafata da su ba.

Kazalika, mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya tabbatarwa Premium Times a hirar wayar tarho a safiyar Lahadi cewar gwamnan ya dauki matakin ne bayan ya yi shawara da masu ruwa da tsaki a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel