Shugaba Buhari na taya China murnanr cika shekaru 69 da zama gurguzu

Shugaba Buhari na taya China murnanr cika shekaru 69 da zama gurguzu

- Najeriya na bin tsarin jari hujja ne a Afirka, Chana na bin na Gurguzu a Asiya

- Kasashen biyu na da alaka ta qut-da-qut musamman a fannin kasuwanci da tattalin arziki

- China ta cika shekaru 69 tun kafuwa a Gurguzu

Shugaba Buhari na taya China murnanr cika shekaru 69 da zama gurguzu
Shugaba Buhari na taya China murnanr cika shekaru 69 da zama gurguzu
Asali: UGC

Kasar Gurguzu ta China, wadda a yau take bikin shekaru 69 tun bayan da Mao Tse Tung, shugaban sojin sa kai na yakar gwamnati ta hanyar tawaye, ya kwace mulki a kasar, ya kori gwamnatin kasar zuwa tsibirin Taiwan, ta tabbata a Gurguzu ne.

Shi dai tsarin gurguzu, ya banbanta da na jari hujja wanda ke mayar da komai na gwamnati, babu wanda ya isa ya mallaki wata kadara, kowacce sana'a ta gwamnati ce.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya kai ziyarar aiki kwanan nan kasar ta Sin, ya samo bashi da kudade masu yawa, wadanda Najeriya ke bukata don manyan ayyukan raya kasa.

DUBA WANNAN: Sai na zarce zaku san me ake kira aiki - Buhari

A wasikar da ya sanya hannu da kansa, Shugaban Najeriya ya taya kasar ta Sin murna, inda ya yaba da yadda take fada da kwarapshan, da kuma yadda ta fiddo da jama'arta da yawa daga qangin talauci wanda a baya yasa yunwa kashe miliyoyi.

Chana dai yanzu ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel