Buhari ya amince kungiyar kasashen musulunci ta taimaka ma Najeriya a yaki da Boko Haram

Buhari ya amince kungiyar kasashen musulunci ta taimaka ma Najeriya a yaki da Boko Haram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi maraba da alkawarin da kungiyar kasashen musulunci, OIC, ta dauka na taimaka ma gwamnatin Najeriya wajen yakar kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mashawarcin shugaban kasa ta fannin watsa labaru, Femi Adesina ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, inda yace Buhari ya amsa wannan tayin ne a yayin ganawarsa da shugaban kungiyar, Dakta Youssed Al-Othaimeen a kasar Amurka.

KU KARANTA: Kato bayan kato: Ana gudanar da zaben tsayar da dan takarar shugaban kasa na APC

Buhari ya amince kungiyar kasashen musulunci su taimaka ma Najeriya a yaki da Boko Haram
Buhari da Othaimeen
Asali: Facebook

Buhari da Othaimeen sun yi wannan ganawar ne a gefen taron koli na majalisar dinkin duniya karo na 73 daya gudana a babban ofishin majalisar dake birnin New York na kasar Amurka, inda Othaimeed yayi alkawarin zasu taimaka ma Najeriya ta hanyar bada ingantaccen ilimi ga yan Najeriya.

A nasa jawabin, Buhari ya gamsu da matakin ilimantar da musulmai ingantaccen ilimi kamar yadda OIC ta bayyana, inda yace ilimi ne kadai zai iya warware mummunar akidar Boko Haram, ya kara da cewa matsalar Boko Haram ta yi kamari ne saboda sauyin yanayi da karuwar yawan jama’a.

Buhari yace akwai bukatar a gyara tafkin Chadi dake isar da ruwa ga sama da jama’a miliyan 45 wadanda suka dangana kacokan da aikin noma, kiwon kifi, kiwon dabbobi da dai sauran sana’o’I dake bukatar ruwa.

Shima Othaimeen yace a yanzu haka 'ya'yan kungiyar kasashen musulmai sun yanke hukunci tallafa ma Najeriya ta hanyar yaki da ta’addanci, kuma tuni suka kammala shirin amfani da kayan ayyukansu da cibiyoyinsu wajen samar da wannan taimako.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng