Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa Sunayen Wakilai 2, 677 da za su fidda gwanayen Takara a 2019

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa Sunayen Wakilai 2, 677 da za su fidda gwanayen Takara a 2019

Mun samu cewa nan ba da jimawa ba jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna, za ta wallafa sunayen wakilan ta 2, 677 da su gudanar da zaben fidda gwanayen takara ta kujeru daban-daban a yayin babban zabe na 2019.

A yayin da guguwar siyasa ta kanannade duk wani lungu da sako na kasar nan sakamakon zaben 2019 ke ci gaba da karatowa, jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa sunayen wakilanta 2, 677 a kafofin watsa labarai da za su gudanar da zaben fidda gwani a kwana-kwanan nan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, akwai manema tikitin takara 220 na kujerar gwamnatin jihar da kuma manema tikitin jam'iyyar 53 dake neman kujerun siyasa daban-daban a fadin jihar.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa Sunayen Wakilai 2, 677 da za su fidda gwanayen Takara a 2019
Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa Sunayen Wakilai 2, 677 da za su fidda gwanayen Takara a 2019
Asali: Twitter

Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ya bayyana a ranar Alhamis din da ta gabata, Mista Abraham Catoh ya bayyana cewa, jam'iyyar za ta wallafa sunayen wakilanta da za su gudanar da zaben fidda gwanaye a ranar Lahadi 30 ga watan Satumba.

KARANTA KUMA: Yajin Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago

Catoh ya bayyana cewa, wannan shawara da jam'iyyar ta yanke a halin yanzu na daya daga cikin yarjejeniyar da ta aiwatar yayin taron shugabanninta da ta gudanar a ranar 26 ga watan Satumba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar ta yi wannan yunkuri domin bayyana jajircewarta da kuma kwazo na tabbatar da gaskiya da adalci tare da bai wa kowane manemin takara dama ta baja kolin sa'ar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel