Kiki-kaka: An shiga dakin sulhu tsakanin tsohon gwamna Adamu da gwamna Al-Makura

Kiki-kaka: An shiga dakin sulhu tsakanin tsohon gwamna Adamu da gwamna Al-Makura

- Masu Sarautun gargajiya na jihar Nasarawa sun kira taron sulhu tsakanin gwamna Tanko Al-Makura da Sanata Abdullahi Adamu

- Sai dai gwamna Umaru Al-Makura ya yi gum da bakinsa bayan da ya fito taron a kan cewa ko anyi sulhu ko akasin hakan

- Gwamna Tanko Al-Makura ya saka kwamishinansa ya nemi takarar kujerer Sanata Abdullahi Adamu tare da kafa kwamitin bincike kan wasu ayyuka da ya yi lokacin yana gwamna

Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura da tsohin gwamnan jihar, Sanata Abdullahi Adamu sun yi wata taron sulhu a dakin taro da ke gidan gwamnati a Lafia tare da masu sarautun gargakiya na jihar.

Wata majiya kwakwara ta ce masu sarautun gargajiyar ne suka kira taron domin sulhunta tsakanin Gwamna Al-Makura da Sanata Abdullahi Adamu musamman a wannan lokacin da jam'iyyar ke gab da gudanar da zaben fitar da gwani.

Kiki-kaka: An shiga dakin sulhu tsakanin tsohon gwamna Adamu da gwamna Al-Makura
Kiki-kaka: An shiga dakin sulhu tsakanin tsohon gwamna Adamu da gwamna Al-Makura
Asali: Twitter

A cikin 'yan kwanakin nan ne Gwamna Al-Makura ya zabi Injiya AA Sule a matsayin mataimakinsa da za suyi takarar tare a zaben fitar da gwani da za ayi a ranar Asabar mai zuwa.

DUBA WANNAN: Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Kazalila, Gwamna Al-Makura ya dauko kwamishinansa na Ilimi, Alhaji Aliyu Tijani domin ya yi takarar kujerer Sanata a Yankin Nasarawa ta Yamma da Sanata Abdullahi Adamu ke wakilta.

Bayan taron, Gwamna Al-Makura, Sanata Abdullahi da masu sarautun gargajiya sun dauki hotuna tare da fuskokinsu cike da murmushi wanda hakan ke nuna alaman sulhu a tsakaninsu amma ba bu tabbas din hakan.

Sai dai Gwamna Al-Makura ya shaidawa manema labarai cewa ba zaiyi tsokaci kan abinda ya wakana a taron ba duk da cewa sun kwashe sa'o'i suna jira a kammala taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel