Wasika ga masu kirga gero a jihar Kebbi, yadda ake kirga irin haka a kimiyyance cikin sauki

Wasika ga masu kirga gero a jihar Kebbi, yadda ake kirga irin haka a kimiyyance cikin sauki

- Musu ya kaisu ga kidayar kwayoyin dake cikin buhun gero

- An yaba wa samarin kan jajircewarsu

- Masana kimiyya na basu shawara kan yadda ake irin wannan aiki

Wasika ga masu kirga gero a jihar Kebbi, yadda ake kirga irin haka a kimiyyance cikin sauki
Wasika ga masu kirga gero a jihar Kebbi, yadda ake kirga irin haka a kimiyyance cikin sauki
Asali: Facebook

Labarin da tashar VOA ta baya na samari a jihar Kebbi na ta zagayawa a shafukan sada zumunci a Najeriya, inda musu ya kaisu har suka shafe watanni biyu suna kidayar yawan kwayoyin gero dake buhu guda, wai ko ya kai yawan 'yan Najeriya.

Matasan sun sami goyon baya sosai a sassa daban daban na kasar nan, ciki harda sarakuna da matasa na sauran yankuna, inda ake yaba jajircewarsu da ma kyautatuwar niyyarsu.

DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari

Sai dai, abin da masana suka hango shine, yadda ake irin wannan aiki a kimiyyance cikin sauki, ya shafe dk wata hanya da wahal da kai da bata lokaci.

Cikin hanyoyi masu sauki, akwai abin da ake kira Sampling, inda zasu kidaya kwano nawa ne a buhu daya, sai su kidaya wadanda suke kwanon guda, sai kawai su ninninka zuwa yawan kwanukan.

Misali: In akwai kwano 40 a buhu daya, kuma akwai kwayar gero 400,000 a kwano daya, ya zama kenan akwai kwayar gero 400,000 sau 40, wato 400,000 X 40 = 16,000,000.

Akwai kuma wasu hanyoyin daban, yi tunani kaima ko kema ki kawo agaji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel