Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna

Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna

A kokarin cigaba da inganta aiyukanta na yaki da ta'addanci, hukumar sojin sama ta kasa (NAF) ta bude wani katafaren dakin binciken laifuka ta hanyar ilimin kimiyya a Ikeja dake jihar Legas.

Bayan binciken laifuka, dakin gwaje-gwajen zai zama cibiyar bayar da horo ga jami'an sojin sama a bangaren kwarewa da dabarun kimiyyar zamani wajen gudanar da binciken laifuka.

A jawabinsa, Ibrahim Idris, Sifeton rundunar 'yan sanda ta kasa kuma babban bako mai jawabi a wurin taron bude dakin binciken, ya yabawa shugaban hukumar sojin, Air Marshal Sadique Abubakar, bisa namijin kokarin da yayi na samar da irin wannan cibiyar bincike ta zamani.

Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna
Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya
Asali: Facebook

Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna
katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya
Asali: Facebook

A nasa jawabin, Air Marshal Abubakar, ya bayyana cewar akwai bukatar samar da cibiyar gudanar da bincike irin na zamani domin samun saukin binciken laifuka.

Abubakar ya kara da cewar tun kafin bude dakin binciken, hukumar sojin sama tare da hadin gwuiwar turawan kasar Ingila dake da kwarewa a fannin bincike ta hanyar amfani da kimiyyar, ta bawa sojoji 16 horo a kan yadda ake amfani da kayan aikin cibiyar domin gudanar da bincike.

DUBA WANNA: Adawa da tazarcen Buhari: Mutumin da ya yi tattaki daga Legas ya iso Abuja

Kazalika, Abubakar ya yi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa irin goyon baya da gudunmawar da yake bawa bangaren tsaro.

Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna
Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya
Asali: Facebook

Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna
Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya
Asali: Facebook

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel