Gwamnonin APC 10 dake neman tazarce a zaben 2019

Gwamnonin APC 10 dake neman tazarce a zaben 2019

A yayin da a ranar Alhamis din da ta gabata ne jam'iyyar APC ta tantance manema takarar kujerun gwamnoni na jihohin kasar nan a shelkwatar dake garin Abuja, Legit.ng ta kawo muku jerin goma dake neman tazarce na kujerun.

Ko shakka ba bu akwai kimanin gwamnoni goma na jam'iyyar da za su kammala wa'adinsu karo na farko bayan samun nasara a zaben 2015, sun kuma bayyana kudirin su na sake neman kujerun karo na biyu dangane da gabatowar babban zabe na 2019.

Gwamnonin dake neman tazarce akan kujerunsu yayin zaben da aka kayyade zai gudana a watan Fabrairun 2019 sun hadar da na jihohin Kebbi Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Neja, Filato, Bauchi, Adamawa da kuma na jihar Legas.

Gwamnonin APC 10 dake neman tazarce a zaben 2019
Gwamnonin APC 10 dake neman tazarce a zaben 2019
Asali: Depositphotos

Ga jerin sunayen Gwamnonin kamar haka: Abubakar Atiku Bagudu, Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru, Aminu Bello Masari, Nasir El Rufa'i, Muhammad Sani Bello, Simon Lalong, Muhammad Abubakar, Jibrilla Bindo da kuma Akinwunmi Ambode.

Akwai kuma jerin wasu gwamnoni na jam'iyyar da ba su da wannan dama ta sake neman kujerun su sakamakon kammala wa'adi da kundin tsarin mulki ya ba su dama na shekaru takwas da suka shafe kan karagar mulki.

Gwamnonin sun hadar da; Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, Kashim Shettima na jihar Borno, Ibrahim Geidam na jihar Yobe, Abiola Ajimobi na jihar Oyo da kuma Ibikunle Amosun na jihar Ogun.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Legas a Fadar Villa

Kazalika gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbseola, ya kammala wa'adinsa na shekaru takwas rike da kujerar gwamatin jihar sa, inda a gobe Asabar za a gudanar da zaben gwamna a jihar kamar yadda hukumar zabe ta kasa ta kayyade.

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, shine ya jagoranci kwamitin jiga-jigai na jam'iyyar da suka tantance manema takarar kujerun gwamnan a unguwar Asokoro dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Shugabannin jam'iyyar sun kuma tantance wasu gwamnoni dake neman tikitin takarar kujerun Sanata na mazabun jihohin su da suka hadar da; Gwamna Abdulaziz Yari, Kashim Shettima, Abiola Ajimobi, Tanko Al Makura na jihar Nasarawa da kuma Rochas Okorocha na jihar Imo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel