Duk kanwar ja ce: Tsohon shugaban PDP da ya fita daga APC ya fadi matsalar manyan jam’iyyun

Duk kanwar ja ce: Tsohon shugaban PDP da ya fita daga APC ya fadi matsalar manyan jam’iyyun

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Barnabas Gemade, ya caccaki jam’iyyar adawa ta PDP da takwararta ta APC, tare da bayyana cewar dukkan jam’iyyun na ‘yan wuru-wuru ne, a saboda haka ya yanke shawarar komawa jam’iyyar SDP.

Da yake Magana da manema labarai a jiya, Gemade, ya ce dalilin day a raba shi da tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP shine ya saka shi fita daga APC, yana mai bayyana cewar babu siyasar ‘yanci ko ta cigaba a dukkan manyan jam’iyyun.

A cewar Gemade, dukkan jam’iyyun basa mutunta tsarin mulikn Najeriya balle su yi aiki da abinda yake kunshe cikin kundin tsarinsu.

Sanata Gemade ya bayyana cewar rashin shugabanci mai ma’ana karkashin gwamnan Benuwe, Samuel Ortom, ne ya haddasa rashin zaman lafiya a jihar.

Duk kanwar ja ce: Tsohon shugaban PDP da ya fita daga APC ya fadi matsalar manyan jam’iyyun
Barnabas Gemade
Asali: Twitter

A ranar litinin ne tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Barnabas Gemade, ya sanar da canjin shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP.

Gemade na daya daga cikin sanatocin jam’iyyar APC da a kwanakin baya suka canja sheka zuwa PDP.

DUBA WANNAN: Daga karshe: IBB ya ware mutum guda da zai goyawa baya a cikin 'yan takarar PDP

Da yake bayar da dalilin ficewarsa daga PDP, Gemade, ya bayyana cewar ya fita ne sabod cin amnarsa da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya yi a kan batun tikitin takarar sanatan gabashin jihar Benuwe.

Yanzu haka Gemade ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan Najeriya bayan komawarsa jam’iyyar SDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel