Yan bindiga sun yi garkuwa da manyan Malamai guda 3 a jahar Kaduna

Yan bindiga sun yi garkuwa da manyan Malamai guda 3 a jahar Kaduna

Wasu malaman kwalejin horas da ma’aikatan kiwon lafiya ta jahar Kaduna dake garin Makarfi guda uku sun fada hannun yan bindiga masu garkuwa da mutane, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito barayin mutanen sun sace Malaman ne a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar dake garin Makarfi daga garin Zaria, haka zalika malaman sun hada da Rabi Dogo, Halimatu Malam da wani babban daraktan makarantar Dakta Akawo.

KU KARANTA: Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar

Dayake tabbatar da lamarin, wani Malami a makarantar, Ahmed Rahama ya bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da Malaman ne da yammacin ranar Lahadi 16 ga watan Satumba.

“Muna cikin bakin ciki da alhini, sashin karatun kimiyyar hakora na kwalejin ya yi wasu baki daga kungiyar likitocin hakora na kasa, wanda aka saukesu a wani otal dake Zaria.

“Wannan ne yasa Malamanmu suka iskesu a Zaria inda suka tattauna, Sun kammala tattaunawar a hanyarsu ta dawowa daga Makarfi daga Zaria ne aka sacesu” Inji Rahama.

Malamain yace yan bindigan sun saka Malaman ne a cikin motarsu, inda suka ajiye motar daraktan akan hanyar da zata shigo da kai garin Makarfi, wanda a yanzu haka Yansanda sun dauke motar daga kan hanya.

Ayyukan satar mutane tare da yin garkuwa dasu ba sabon abu bane a jahar Kaduna, inda a lamarin ya fi ta’azzara a yankunan Birnin Gwari da kuma babbar hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna yaci tura.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel