An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna

An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna

- Majalisar Jihar Kano za tayi zaman tantance Nasir Yusuf Gawuna a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano

- Gwamna Ganduje ya zabi Yusuf Gawuna ne domin cikin gurbin da tsohon mataimakin gwamnan Hafiz Abubakar ya bari bayan ya yi murabus

- A yanzu, Nasir Yusuf Gawuna shine kwamishinan Ayyukan Noma da Albarkatun kasa a jihar ta Kano

Majalisar Jihar Kano ta tsayar Talata 18 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta tantance kwamishinan Ayyukan Noma, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin mataimakin gwamna Abdullahi Ganduje na jihar.

An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna
An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna
Asali: Twitter

Nasir Yusuf Gawuna zai bayyana a gaban majalisar ne misalin karfe 10 na safiya.

DUBA WANNAN: Tawagar gwamnan APC tayi hatsari a hanyar zuwa Abuja

Idan majalisar ta amince da nadin sa, Gawuna zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamna Hafiz Abubakar da ya yi murabus a ranar 9 ga watan Augustan shekarar 2018.

A wasikar da gwamna Abdullahi Ganduje ya aike wa Kakakin majalisar jihar, Kabiru Rurum wadda aka karanta a gaban majalisar a jiya Litinin, gwamnan ya ce ya rubuta wasikar ne kamar yadda sashi na 191 (3) (c) na kundin tsarin Najeriya na 1999 ya tanada.

Gwamna Ganduje ya yi fatan cewa majalisar za ta bashi hadin kai wajen tantancewa da amincewa da Nasiru Gawuna a matsayin mataimakinsa.

Kafin nadinsa, Gawuna shi ne kwamishinan ma'aikatan ayyukan Noma da Albarkatun kasa kuma mamba ne Kwamitin Zartarwa na Jihar Kano. Ana sa ran zai kama aiki nan take idan majalisar suka tantance shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164