Gwamnatin Kaduna na bukatar N70bn domin wani muhimmin aiki a bangaren Ilimi

Gwamnatin Kaduna na bukatar N70bn domin wani muhimmin aiki a bangaren Ilimi

- Wani ma'aikaci a Hukumar Kula da Ilimin Frimari (SUBEB) ya ce suna bukatar N70bn domin gyara dukkan makarantun frimare na jihar

- Jami'in ya ce kudaden da hukumar ke samu daga gwamnatin jihar da UBEC ba zai isa ayi wadandan gyare-gyaren ba

- Ya ce gwamnatin jihar na iya kokarinta na inganta ilimi a jihar duk da cewa kudaden da take dashi basu wadatar ba

Wani kwararen mai nazarin gine-gineda ke aiki da Hukumar Kula Ilimin Frimari (SUBEB), Mr Jonathan Joseph, ya ce hukumar na bukatar a kalla N70 biliyan domin gyaran makarantun frimare na gwamnati fiye da 4,200 a jihar.

Gwamnatin Kaduna na bukatar N70bn domin wani muhimmin aiki a bangaren Ilimi
Gwamnatin Kaduna na bukatar N70bn domin wani muhimmin aiki a bangaren Ilimi
Asali: Depositphotos

Joseph ya yi wannan maganar ne a yau Litinin yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a wajen wani taron wayar da kan shugabanin kafafen yada labarai kan hanyoyin da za su inganta watsa ayyukan hukumar.

DUBA WANNAN: Tawagar gwamnan APC tayi hatsari a hanyar zuwa Abuja

Wata kungiya zai kai, Legal Awareness for Nigerian Women na ta shirya taron domin neman taimakon 'yan jarida wajen sanya idanu kan ayyukan da SUBEB keyi a fanin ilimi a jihar.

Joseph ya ce an cimma matsaya kan adadin kudin bayan an gudanar da bincike mai zurfi shekaru biyar da suka shude domin gano yawan kudin da ake bukata muddin ana son inganta gine-gine a dukkan makarantun frimare na gwamnati da ke jihar.

Jami'in ya ce hukumar ta samu N2 biliyan da N2.5 biliyan duk shekara daga UBEC da kuma gwamnatin jihar Kaduna cikin shekaru uku da suka gabata sai dai wadandan kudaden ba za su wadata ayi dukkan ayyukan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel