2019: Kungiyar Kiristoci ta goyi bayan Buhari

2019: Kungiyar Kiristoci ta goyi bayan Buhari

- Kungiyar matasan Kirista na jihar Akwa Ibom sun bayyana goyon bayansu ga Buhari a zaben 2019

- Sun koma goyi bayan, shugaban NDCC, Mr Nsima Ekere a matsayin gwamna a karashin APC a jihar

- Matasan sunyi wannan albishir din ne a wata taro da suka kira a filin matsa jiki a birnin Uyo

Matasa mabiya addinin Kirista na jihar Akwa Ibom karkashin kungiyar Christain Youths Leaders Assembly, sun goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari da Mr Nsima Ekere, babban manajan hukumar Neja-Delta (NDCC) a matsayin 'yan takarar shugabancin kasa da gwamna a karkashin jam'iyyar APC a 2019.

2019: Kungiyar Kiristoci ta goyi bayan Buhari
2019: Kungiyar Kiristoci ta goyi bayan Buhari
Asali: Twitter

Matasan sun bayyana goyon bayansu ga 'yan takarar biyu ne a wata gangami da suka shirya a filin motsa jiki na Uyo wanda ya samu hallarcin mambobin kungiyar daga mazabu 329 da kauyuka 2,273 da ke jihar.

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Wakilin shugaba Buhari a wajen taron, Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a fannin harkokin majalisa, Sanata Ita Enang, ya yi godiya ga matasan kan goyon bayan da suka bawa 'yan takarar biyu, ya kuma ce suyi amfani da dokar rage shekarun zabe da shugaba Buhari ya amince da ita su shiga siyasa a dama da su.

A jawabinsa, Ekere ya yabawa matasan saboda irin matakin da suka dauka sabanin wasu shugabanin kirista da suka zabi hanyar yada kiyaya tsakanin mutanen Najeriya.

"A yau, kun wanke addinin kirista daga zargi. Kafin zuwa na wajen taron na, na samu labarai da yawa inda aka ce shugabanin addinin Kirista sun rikide sun zama 'yan siyasa suna bin coci-coci suna yada kiyaya." inji Ekere.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel