Mayakan wani reshe na Boko Haram sun kashe Shugabansu, Mamman Nur

Mayakan wani reshe na Boko Haram sun kashe Shugabansu, Mamman Nur

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, shugaban reshen kungiyar Boko Haram wanda ya yiwa kungiyar ta'adda ta IS mubaya'a a yankin Afirka ta Kudu, Mamman Nur, ya gamu da ajali a hannun mayakansa da suka juya ma sa baya.

Majiyoyi dake da ingantacciyar masaniya akan kungiyar ta'addan sun shaidawa manema labarai na jaridar Daily Trust wannan rahoto da cewa, Nur wanda shine ya kulla alakar kungiyar Boko Haram da kuma kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi ta IS, ya gamu da ajali a hannun mayakansa a ranar 21 ga watan Agustan da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun a shekarar 2014 da ta gabata ne Marigayi Nur ya raba kan kungiyar ta Boko Haram, inda ya hada dakarunsa da suka juya baya akan Abubakar Shekau da a sanadiyar hakan aka samu wani reshe na kungiyar bisa jagorancin Abu Mus'ab Al-Barnawy.

Al-Barnawy, sabon shugaban kungiyar wanda ainihin sunan sa Habib, ya kasance ɗa ga shugaban kungiyar Boko Haram tun na fil azal, Marigayi Muhammad Yusuf da dakarun sojin Najeriya suka kar shekaru 9 da suka gabata.

Dakarun Sojin Najeriya a bakin aiki
Dakarun Sojin Najeriya a bakin aiki
Asali: Facebook

Binciken manema labarai ya bayyana cewa, mayakan na Marigayi Nur sun juya baya a gare sa ne bayan tsawon shekaru da suka shafe na sabani tsakanin sa da su kan cewa ya kauce daga kan tafarkin da suka kafu a kai.

Legit.ng ta fahimci cewa, sabanin ya auku ne a yayin da mayakan ke ganin shugaban su ya na da rauni kasancewar bai kai Shekau zafi ba ta fuskar batar da duk wani mahaluki walau Musulmi ko Kafiri da ya sabawa tsari da akidu irin na sa ra'ayin na addini.

Daya daga cikin manyan sabani da Marigayi Nur ya samu da mayakansa ya auku ne a sanadiyar sako 'yan Mata 100 na makarantar garin Dapchi dake jihar Yobe a watan Maris din da ya gabata.

KARANTA KUMA: PDP ce za ta yi nasara a Zaben 2019 - Kwankwaso

Sai da kawowa yanzu hukumar sojin Najeriya ba ta tabbatar da wannan rahoto na kisan Mamman Nur ba, inda a ranar 6 ga watan Janairun da ta gabata ta bayar da tabbacin salwantar rayuwar Uwargidan sa yayin wani simame na dakarun sojin da ya ritsa da ita a gabar tafkin Chadi.

Kazalika, kakakin rundunar soji ta Lafiya Dole dake birnin Maiduguri, Onyeama Nwachukwu, ya bayyana cewa a baya kadan mayakan Boko Haram kimanin 250 da suka yiwa Marigayi Mamman mubaya'a sun saduda yayin da tura ta kai bango.

A yayin haka jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa, a watan Satumban shekarar 2011 da ta gabata ne hukumar tsaro ta DSS ta sanya tukwicin N25m kan duk wanda ya kawo ma ta Mamman Nur a mace ko a raye bayan harin da mayakan sa su kai ofishin majalisar dinkin duniya dake garin Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel