2019: Jami’in kwastam mai ritaya Ibrahim Mero ya shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi

2019: Jami’in kwastam mai ritaya Ibrahim Mero ya shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi

- Mataimakin Kwanturola Janar na Kwastam mai ritaya, Ibrahim Mohammed Mera, ya shiga tseren takarar gwamna a jihar Kebbi

- Mera zai yi takara ne a karkashin jam'iyyar APC

- Jami'in kwastam din yayi suna kafin yayi ritaya lokacin da yaki karban cin hanci sama da naira biliyan 1 da wasu masu fasa kauri suka bashi

Mataimakin Kwanturola Janar na Kwastam mai ritaya, Ibrahim Mohammed Mera, ya shiga tseren takarar gwamna a jihar Kebbi karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mera ya yayi suna sosai a lokacin da yake kwanturolan kwastam na yankin Kano/Jigawa lokacin da ya jagoranci jami’ansa zuwa yankin Sharada na jihar Kano don damke wasu masu fasa kauri na sinkin shaddodi guda 253,000 da kudinsu ya kai naira biliyan 4.

An rahoto cewa yaki amsar cin hancin sama da naira biliya guda wadda masu fasa kaurin suka basa sannan sunan aikin SHARADA SMASH, ya kafa tarihi a hukumar kwastam.

2019: Jami’in kwastam mai ritaya Ibrahim Mero ya shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi
2019: Jami’in kwastam mai ritaya Ibrahim Mero ya shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa shigar Mera takarar gwamna ya haifar da hatsaniya a siyasar jihar saboda shararsa.

Mera ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamna a ranar Talata, 29 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar NLC ta ki amincewa da Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasa

Ya bayyana kudirin nasa a gidansa dake Abuja yayinda ya karbi bakuncin abokai, hadimai da magoya bayansa wadanda suka bukaci ya shiga tseren.

Yace ya shiga tseren ne domin yayiwa al’umman jiharsa aiki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel