2019: Sanata, tsohon gwamna da DIG mai ritaya sun koma APC a jihar PDP

2019: Sanata, tsohon gwamna da DIG mai ritaya sun koma APC a jihar PDP

- Sanata mai ci, tsohon mataimakin gwamna da tsohon mataimakin shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (DIG) sun koma APC a jihar Akwa Ibom

- 'Yan siyasar sun fita daga jam'iyyar PDP ne a jiya, Talata

- Dukkan 'yan siyasar sun koma jam'iyyar ta APC ne tare da magoya bayansu

Sanata mai wakiltar jihar Akwa Ibom ta kudu, Eme Ekaette, da Valerie Ebe, tsohon mataimakin gwamnan jihar, sun canja sheka daga PDP zuwa APC a jiya, Talata, 11 ga watan Satumba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar daga cikin wadanda suka canja shekar zuwa APC akwai tsohon mataimakin rundunar 'yan sanda na kasa, Udom Ekpoudom da tsohon shugaban karamar hukumar Eka, Francis Ikpon.

Shugaban jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom, Ini Okpobodi, ne ya karbi 'yan siyasar a wani taron gangami da APC tayi jiya, Talata, a karamar hukumar Eket.

2019: Sanata, tsohon gwamna da DIG mai ritaya sun koma APC a jihar PDP
Magoya bayan APC a wurin taron APC a jihar Akwa Ibom
Asali: Depositphotos

Okpobodi ya mika manyan 'yan siyasar ga Hillary Eta, mataimakin shugaban APC na kasa kuma wakilin shugaban jam'iyyar na kasa a wurin taron.

A jawabinsa, Eta ya ce an fuskanci matsi bayan hawan shugaba Buhari amma yanzu abubuwa na yin sauki.

Kazalika ya bukaci jama'a dasu fito kwai da kwarkwata domin zazzagawa shugaba Buhari kuri'a a zaben 2019.

DUBA WANNAN: 2019: Tinubu ya tsayar da sabon dan takarar gwamna a jihar Legas, ya juyawa Ambode baya

A wani labarin na Legit.ng, kun karanta cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa.

A karshe, Malam Ibrahim Shekarau, ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa ta Giginyu a karamar hukumar Nasara dake Kano a ranar Lahadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel