Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna

Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna

Batun zaben 'yan tinke ya taso a jam'yyar APC inda wasu ke ganin idan ba'a yi zaben fidda gwani ba na kato bayan kato to babu adalci domin idan akayi amfani da wakilai wajen zaben za'a iya samun wasu 'yan takarar da za suyi amfani da kudi domin ganin sun lashe zaben.

Sanata Shehu Sani da wasu masu neman takara 14 karkashin jam'iyyar APC na jihar Kaduna sun ki amincewa da tsarin amfani da wakilai wajen zaben fitar da gwani kamar yadda jam'iyyar ta bukaci a yi.

'Yan takarar sunyi korafi a wata wasika da suka aike wa Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole inda suka nemi a yi amfani da tsarin kato bayan kato.

Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna
Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna
Asali: Depositphotos

A cewarsu, amfani da wakilai ya ci karo da yunkurin da shugaba Muhammadu Buhari keyi na yaki da rashawa a dukkan bangarorin rayuwar 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Abinda ya farraka ni da Shekarau – Takai

'Yan takarar sunyi korafin cewa amfani da wakilai zai bawa wasu 'yan takarar damar amfani da kudi wajen sayan wakilan a maimakon a bari kowanne dan takara halinsa ya cece shi

Bayan Sanata Shehu Sani (Kaduna Central), wani mai neman takarar gwamna a jihar Kaduna, Halalu Falalu shima ya saka hannu a wasikar.

Sauran sun hada da Mohammed Sani, mai neman takarar Sanata a Kaduna Central ta tsakiya, Aliyu Silver, mai neman takarar Sanata a Kaduna Kaduna ta Arewa da Rufai Chanchangi, dan majalisa mai wakiltan Kudancin Kaduna a majalisar dattawa.

Idan ba'a manta ba, Legit.ng ta ruwaito cewa Kwamitin zartawar ta APC ta yanke shawarar amfani da tsarin kato bayan kato a zabukan fidda gwani na tarayya sai dai ta bawa jihohi zabin amfani da wani tsarin idan 'yan jam'iyyar sun amince.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel