Sojoji sun rugurguza wasu gine-ginen Boko Haram a dajin Sambisa

Sojoji sun rugurguza wasu gine-ginen Boko Haram a dajin Sambisa

- Sojin Saman Najeriya (NAF) sun sake samun gagarimin galaba kan mayakan Boko Haram a Borno

- Dakarun Sojin Saman sunyi luguden wuta a wata mafakar 'yan Boko Haram da ke Alafa Yagayaga

- Har ila yau, Sojin sun sake samun nasarar kai sumame tare da lalata dakin ajiyar makaman 'yan ta'addan a Kusuma

Hukumar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa dakarunta na rundunar Operation Lafiya Dole sunyi nasarar halaka wasu mayakan Boko Haram tare da lalata kayayakinsu a wata mafakarsa da ke Alafa Yagayaga a dajin Sambisa.

A cewarsa Hukumar Sojin Saman, Sojojin sun kuma yi luguden wuta a wani ma'ajiyar makamai na Boko Haram da ke Kusuma a kusa da iyakar Tafkin Chadi.

Sojin Saman Najeriya sun sake samun babban galaban kan 'yan Boko Haram
Sojin Saman Najeriya sun sake samun babban galaban kan 'yan Boko Haram
Asali: Facebook

Wannan sanarwan ya fito ne daga bakin Direktan yada labarai na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, a wata sako da ya fitar a yau Abuja.

DUBA WANNAN: Sojojin Najeriya sun tsare wani dan majalisa a kan rikicin jihar Filato

Ya ce an kai hare-haren saman ne saboda cigaba da atisayen Operation Thunder Strike 2 da hukumar sojin ta faea a ranar 3 ga watan Satumba.

"An kai harin sama a mafakar mayakan Boko Haram a Alafa Yagayaga ne sakamakon bayyanan sirri da suka bayyana cewa akwai mafakar da 'yan ta'addan ke taruwa.

"Bayan haka, anyi amfani da jiragen yakin NAF da kuma jirage masu saukan ungulu masu dauke da bindigogi domin karasa kashe burbushin 'yan ta'addan da suka rage," inji shi.

Daramola kuma ya ce an kai sumame a Kusuma bayan an samu bayani daga majiya kwakwara cewar mayakan Boko Haram na ajiye makamansu da motocci a wajen.

Ya ce an kuma rusa wasu gine-gine da 'yan ta'addan ke amfani dasu duk a cikin hare-haren da aka kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel