Yansanda sun buɗe ma wani barawon mutane wuta yayin da zai amshi kudin fansa

Yansanda sun buɗe ma wani barawon mutane wuta yayin da zai amshi kudin fansa

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wani matashi mai suna Yunusa Musa da ya shahara wajen satar mutane, tare da yin garkuwa dasu har sai an biya shi kudin fansa, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kama Yunusa ne a daidai lokacin da yake kokarin amsan kudin fansa daga iyayen wata yarinya Nana da ya saceta daga unguwar Guga Bakori, ya kuma yi garkuwa da ita.

KU KARANTA: Mazauna birnin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare

Kaakakin Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace Yunusa ya nemi a kai masa kudin fansa zuwa dajin Pauwa dake cikin karamar hukumar Kankara, daga nan sai DPO na Yansandan yankin ya jagoranci tawagar Yansanda zuwa dajin don ceto yarinyar.

A kokarinsa na fitowa ya dauki kudin ne sai Yansanda suka bude masa wuta, inda a yanzu haka yana babban asibitin garin Kanakara yana samun kulawa, kuma tuni aka mika Nana ga iyayenta.

“A ranar 3 ga watan Satumba ne DPA na Yansandan Kankara ya jagoranci ceto wata karamar yarinya da wani mutumi yayi garkuwa da ita, inda ya nemi a kai masa kudin fansan daya nema zuwa dajin Pauwa.

"Amma bai samu nasara ba inda Yansanda suka bude masa wuta a daidai lokacin da yayi kokarin daukan kudin fansan. A yanzu haka yana asibitin Kankara yana samun kulawa, ita kuwa karamar yarinyar an mikata ga hannun iyayenta bayan duba lafiyarta a Asibiti.” Inji SP Gambo Isah.

Daga karshe kaakakin Yansandan yace tuni rundunar ta kaddamar da bincike game da lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel