Kungiyar da ta biya ma Buhari kudin takara ta bara: Babu wani jami’in gwamnati daya bamu kwandala

Kungiyar da ta biya ma Buhari kudin takara ta bara: Babu wani jami’in gwamnati daya bamu kwandala

Tun bayan da wata kungiyar matasa ta biya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kudin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka kai naira miliyan arba’in da biyar, an yi ta samun cece kuce, da ra’ayoyi mabanbanta game da hakan.

Legit.ng ta ruwaito sunan wannan kungiya mai rajin ganin shugaba Buhari ya zarce itace “National Consolidation Ambassadors Network” kuma yayanta sun fito daga sassan kasarnan daban daban.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta yi watsi da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

Shugaban wannan kungiya, Barista Sunusi Musa yayi karin haske game da yadda suka tara wadannan makudan kudade, inda yace sun kwashe shekara daya suna shirya wannan lamari, kuma babu wani jami’in gwamnati daya basu koda kwandala daga cikin wannan kudi.

Kungiyar da ta biya ma Buhari kudin takara ta bara: Babu wani jami’in gwamnati daya bamu kwandala
Sunusi
Asali: Facebook

“Wani mutumi dan kasuwa daga kabilar Ibo ne kadai na san ya bamu gudunmuwar naira miliyan biyar bayan ya samu labarin manufarmu, amma babu wani jami’in gwamnati daya bamu ko kwabo. Mun gamsu da salon mulkin Buhari ne, don haka muka yanke shawarar goya masa baya.” Inji shi.

Kungiyar da ta biya ma Buhari kudin takara ta bara: Babu wani jami’in gwamnati daya bamu kwandala
Kudin
Asali: Facebook

Idan za’a tuna a gabanin zaben shekarar 2014, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wani katin neman taimako don taimaka ma yakin neman zaben Buhari da kudade, wanda jama’a suka dinga saya, har karewa suka dinga yi.

Sai dai ba lallai bane jama’a su sake tara ma Buhari kudi a yanzu dayake shugaban kasa, musamman yadda ra’ayin jama’an kasar ya rabu biyu akansa, a yayin da wasu ke san barka, wasu kuma suna Alatsine.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel