Wata mace Kirista ta zama gwamna a kasar Misra a karon farko
Shugaba Abdel-Fattah al-Sissi na kasar Masar ya rantsar da sabbin gwamnoni 12 cikinsu har da gwamna mace na farko a jihar wadda ta fito daga mabiya addinin kirista marasa rinjaye a jihar.
An rantsar da Manal Mikhail a matsayin gwamnan jihar Damietta, wannan na nuna Mikhail ta kafa tarihi a matsayin mace Kirista ta farko da ta fara rike wannan matsayin kamar yadda al-Masry al-Youm ta ruwaito.
Kafin a nada ta gwamna, macen mai shekaru 51 ta rike mukamin mataimakiyar gwamna a Giza, garin da husumiyar Masar suke.

Asali: Twitter
Kasar Masar ce ke da adadin mabiya addinin Kirista mafi yawa a cikin kasashen gabas ta tsakiya. Adadin mabiya addinin Kirista a Masar ya kai 10% cikin adadin mutane 95 miliyan da ke kasar.
DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa
Mabiya addinin kirista a Masar sun dade suna kokawa kan wariya da matsin lamba da musulmi ke musu a kasar.
Al - Sissi duk da cewa musulmi ne yana da farin jini a wajen mabiya addinin Kirista a kasar. Ya goyi bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi bayan jama'a sunyi zanga-zanga bisa salon mulkinsa na raba kan jama'a.
Al-Sissi yana kusantar mabiya addinin Kirista a kasar musamman idan akayi la'akari da cewa ya kai ziyara da dama zuwa babban Cocin kasar da ke Cairo duk bayan hawansa mulki a shekarar 2014.
A shekarar 2016, magoya bayan al-Sissi sun amince da kudirin dokar sassauta dokokin neman izinin gina Coci a kasar wanda aka dade ana neman majalisar ta amince da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng