Kwankwaso yayi karin haske kan dalilin bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa

Kwankwaso yayi karin haske kan dalilin bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana babban dalilin fitowarsa takarar shugaban kasa karo na biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, kamar yadda gidan rediyon bbc hausa ta ruwaito shi.

Kwankwaso ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa ya fito takara ne don taimakon yan Najeriya, musamman game da abinda ya shafi ayyukan titiuna, da dukkanin ayyukan daya kamata wani yayi, ko a harkar ilimi.

KU KARANTA: Buhari ya sahhale ma wani Ministansa ya tsaya takarar gwamnan wannan jahar

Kwankwaso ya cigaba da cewa ba shi ba ma kadai, jama’a da dama na ganin shi yafi cancanta da kujerar shugaban kasa, “Cikin yardar Allah, wannan ne ya bamu kwarin gwirar fitowa neman wannan kujera.” Inji shi.

Kwankwaso yayi karin haske kan dalilin bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa
Kwankwaso
Asali: Facebook

Da aka tambayeshi game da sauran yan takarar shugaban kasa a PDP, sai yace: “Indai cancanta ake bi ta harkokin siyasa da kuma kwarewa a harkokin ayyukan gwamnati, toh bama ni na sauran jama’ana ganin ni nafi cancanta jam’iyya ta tsayar dani don ganin PDP ta samu nasara.”

Bugu da kari Kwankwaso yace jama’a na da dama yi ma burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa fassara daban daban, toh amma a cewarsa kowa ya san halin da ake ciki a wannan gwamnati, “Akwai bukatar canza salo don mun a samu cigaba a wannan kasa.”

Daga karshe yace mai yiwuwa ne su daidaita da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau game da batun tasa bukatar da tsayawa takarar shugaban kasa, “Ba mamaki kuma mu tafi har ga zaben fidda gwani sai mu hadu mu yi aiki tare ga duk wanda Allah ya ba.

“Harkace ta siyasa, koda na zama gwamnan Kano, banyi wani abu na bata masa rai ba ko ci masa mutunci ba, saboda haka wannan zai taimaka wajen ganin mun hadu mun yi aiki tare.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel