An gudu ba a tsira ba: Wani Gwamna ya gudu daga APC, PDP kuma sun ce baza su ba shi tikitin takara ba

An gudu ba a tsira ba: Wani Gwamna ya gudu daga APC, PDP kuma sun ce baza su ba shi tikitin takara ba

- Alamu na nuna cewar gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom na dab da yin biyu babu

- Domin jam'iyyar da ya gudu domin su bashi tikitin takarar gwamna a karo na biyu wato PDP suna shakkar bashi tikitin

An gudu ba a tsira ba: Wani Gwamna ya gudu daga APC, PDP kuma sun ce baza su ba shi tikitin takara ba
An gudu ba a tsira ba: Wani Gwamna ya gudu daga APC, PDP kuma sun ce baza su ba shi tikitin takara ba

Alamu na nuna cewar gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom na dab da yin biyu babu, domin jam'iyyar da ya gudu domin su bashi tikitin takarar gwamna a karo na biyu wato PDP suna shakkar bashi tikitin takarar a shekarar 2019.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar wa da wakilan cewar jam'iyyar ta yi babban taron shugabannin jam'iyyar a cikin satin nan, inda suka ki amince wa da bukatar gwamnan ta fitowa takara a karo na biyu, da kuma bashi damar shugabantar jam'iyyar a jihar ta Benue.

DUBA WANNAN: Wata yarinya ta kuduri aniyar kare hakkin Fulani

Rahotanni sun nuna cewar shugabannin jam'iyyar na kasa sun hadu da shugabannin jam'iyyar na jihar ta Benue domin tattaunawa akan matsalar gwamnan.

Wani mai neman takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar ta PDP, Tehemen Tarzoor, ya bayyanawa manema labarai cewar, 'yan takarar gwamnan jihar baza su taba yarda jam'iyyar PDP ta bawa Ortom damar shugabantar jam'iyyar a jihar ba, wanda bai jima da canja sheka daga jam'iyyar APC ba.

Saboda haka maganar a bawa gwamna mai ci shugabantar jam'iyyar mu ma bai taso ba. A kyale shi shima ya shigo cikin mu ayi gwagwarmaya dashi. Amma idan har kunce dole zaku bashi to ai akwai kotu zamu je kotu tayi mana shari'a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel