Anyi batakashi tsakanin Dakarun Sojoji da yan bindiga a jihar Kaduna, 5 sun mutu

Anyi batakashi tsakanin Dakarun Sojoji da yan bindiga a jihar Kaduna, 5 sun mutu

Rundunar ta daya ta Sojan kasan Najeriya dake jihar Kaduna tace mayakanta sun bindige wasu yan bindiga guda biyar har lahira a yayin wata musayar wuta da suka dade suna fafatawa a tsakaninsu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Jaridar Preium Times ta ruwaito mataimakin daraktan watsa labaru na runduna ta daya, Muhammad Dole ne ya sanar da haka a yayin ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, inda yace gayyatar Sojoji aka yi.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji

“Mun samu kiraye kirayen jama’a game da ayyukan wasu yan fashi da suka tare hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa, nan da nan Sojoji suka dira yankin, sai dai a yayin da Sojoji ke bin sawun yan fashin, sai wasu yan bindiga suka bude musu wuta a harin kwantan bauna.

“Anan fa aka dinga musayar wuta tsakanin yan bindigan da Sojoji, har sai da Sojoji suka ci karfin yan bindigan, inda suka tsere zuwa dajin Kuyambana dake jihar Zamfara, sa’annan mun gano gawar yan bindiga guda biyar bayan musayar wutar, daga ciki har da Sani Danbuzuwa gagararren dan fashi.” Inji shi.

Muhammad Dole yace an samu mamaci guda daga bangaren Sojoji, da kuma Sojoji biyu da suka samu rauni a sakamakon harin, sai dai yace suna nan suna samun kulawa a Asibitin Sojoji dake garin Kaduna. Daga cikin makaman da Sojoji suka kwato daga yan bindigan akwai bindigar AK 47 guda daya, bindigar G Rifle da alburusai da dama,

Daga karshe majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’im Sojan yace sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane Yunusa Suleiman a ranar 14 ga watan Agusta, kuma a yanzu haka yana taimaka musu da bayanai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel