APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki
- Muna shirye shiryen tsige Saraki daga kujerar shi
- Bazamu yi hakan ba, har sai mun cika dukkanin ka'idoji
- Shawara daya zamu bashi, itace ya sauka tun kafin lokaci ya kure masa
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa tana aiki tare da wasu sanatoci daga jam'iyyar PDP domin shirin tsige shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki.
Mista Yekini Nabena, Mukaddashin sakataren yada labarai na jam'iyyar ne ya bayyana haka.
DUBA WANNAN: Bafarawa: Koda na fadi zaben fidda gwani bazan bar PDP ba
"A matsayin mu na jam'iyya, bamu yarda tirsasa mahukuntan gurin tsige Saraki daga kujerar shi ba. Zamu samu goyon bayan sanatocin PDP domin samun kaso 2 bisa 3 na majalisar. A halin yanzu ma muna magana da sanatocin PDP wadanda suka yarda tare da goyon baya idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kan mulkin shi," inji jam'iyyar.
Jam'iyyar mai mulki ta bukaci Saraki da ya sauka daga kujerar shi ta shugaban majalisar.
"Ba zai iya shugabantar APC mai rinjaye a majalisar ba. Amma Idan yaki sauka da lalama, zamu tsige shi. Farfagandar PDP da barazanar su bazata kare shi ba," ta kara da hakan.
Jam'iyyar ta zargi PDP da yunkurin kai har ga sanatocin APC a matsayin matakin kare Saraki daga sauka kujerar shugaban majalisar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng