Matashin ‘Dan wasan Kasar Amurka ya haifi yara 4 da mata 4

Matashin ‘Dan wasan Kasar Amurka ya haifi yara 4 da mata 4

Da alamu dai karshen Duniya ta zo bayan labarin wani saurayi mai shekaru 18 kacal a Duniya da ke shirin samun yaron sa na 5 a Duniya ya bazu. Wani Bawan Allah mai suna Kgopolo Nphela ya bada wannan labari a makon jiya.

Matashin ‘Dan wasan Kasar Amurka ya haifi yara 4 da mata 4
Young Boy mai shekaru 18 zai samu 'Dan sa na 5 a Duniya

Kgopolo Nphela yayi amfani da shafin sa na Tuwita ya bada labarin wani ‘Dan kwasan kwallon Kwando a Amurka da yanzu yake jiran wata Budurwar sa ta sauka. Ana sa rai Budurwar wannan Saurayi ta haifa masa ‘dan sa na 5 a Duniya.

KU KARANTA: Wata Daliba ta lashe kyaututtuka na ban mamaki

Ko da dai wannan yaro bai kai shekaru 20 a Duniya ba, har ya haifi ‘Ya ‘ya 4 kuma yana jiran saukar na 5 yau ko gobe. Yanzu haka tsohuwar Buduwar wannan shararren Matashi ce mai suna Jania ke dauke da tsohon cikin wani yaron sa.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan Bawan Allah da ya shahara wajen harkar kwallon Kwando ya rabu da Jania kuma har ta kai ba a bari su hadu da juna. Rikicin ya barke ne bayan an zarge sa da lakadawa Buduwar ta sa duka.

Sunan wannan Matashi dai bai bayyana mana ba amma ana masa lakabi da Young Boy. Kawo yanzu ya samu ‘Yan mata har 4 da su kayi ciki su ka haifa masa yara daban-dabam. Wannan saurayi da yayi fice a Amurka bai da aure har yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng