Har ila yau: Tsohon ministan PDP daga arewa ya canja sheka daga PDP zuwa APC

Har ila yau: Tsohon ministan PDP daga arewa ya canja sheka daga PDP zuwa APC

A yau, Laraba, ne tsohon ministan sufuri karkashin gwamnatin PDP, Yusuf Suleiman, ya yanki tikitin zama dan jam’iyyar APC a mazabarsa ta Isa ta kud dake karamar hukumar Isa a jihar Sokoto.

An bashi katin shaidar zama dan jam’iyyar APC mai dauke da lambobin mallaka kamar haka: 381113. Shugaban APC, Alhaji Sadiq Isah Achida, ne ya bayar da katin ga tsohon minister Yusuf a gaban ragowar shugabannin jam’iyyar.

Har ila yau: Tsohon ministan PDP daga arewa ya canja sheka daga PDP zuwa APC

Tsohon minista Yusuf Suleiman

A takaitaccen jawabinsa, Yusuf, y ace “bani da kalmomin d azan yi amfani das u yanzu domin nuna jin dadin irin karramawar da ku ka yi min amma nan bad a dadewa b azan gabatar ga jawabi a kan dawowata APC.”

DUBA WANNAN: Ana kulla tuggun tsige shugaba Buhari - Tinubu

A wani labarin mai alaka da wannan, kun ji cewar kamar yadda mai bawa shugaba Buhari shawara a kan harkokin majalisar dattijai, Ita Enang, ya sanar tun ranar Lahadi cewar a ranar 8 ga wata za a yi bikin karbar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, zuwa jam’iyyar APC, an gabatar da taron bikin a filin wasa na garin Ikot Ekpene.

Manyan 'ya'yan jam'iyyar APC da suka hada da 'yan majalisar wakilai, Sanatoci da shugabannin jam'iyya sun halarci wurin bikin karbar Akpabio.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel