Boko dadi: Wanda yafi kowa cin jarrabawar JAMB a Najeriya ya sami N5m daga gwamnan Borno

Boko dadi: Wanda yafi kowa cin jarrabawar JAMB a Najeriya ya sami N5m daga gwamnan Borno

- Gwamnan jihar Borno ya dau nauyin karatun yaron da ya zama zakaran gwajin dafi na JAMB din shekarar nan

- Israel Zakari Galadima yaci maki 364 a Jarabawar shi ta JAMB, wanda shine yafi kowa maki a kasar

- Daukar nauyin karatun jami'ar shi da akayi na shekaru biyar ya kai kimanin Naira miliyan 5

Boko dadi: Wanda yai kowa cin jarrabawar JAMB a Najeriya ya sami N5m daga gwamnan Borno

Boko dadi: Wanda yai kowa cin jarrabawar JAMB a Najeriya ya sami N5m daga gwamnan Borno

Mun ruwaito labarin wani yaro Dan karamar hukumar Biu, jihar Borno, Israel Zakari, ya samu maki mafi yawa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare na shekarar 2018.

Nan da nan yayi fice a yanar gizo, inda mutane da yawa ke ta yaba hazakar shi.

DUBA WANNAN: Siyasar Najeriya da gwamnatin Tarayya

A haka dai har ta kai ga gwamnan jihar Borno yaji labarin yaron kuma ya yaba. A yanzu dai ya dau nauyin karatun shi na shekara 5,inda zai karanci fannin Electrical Engineering a jami'ar Covenant dake Ota, jihar Ogun.

Mun samu labarin ne bayan da Gwamna Shettima ya gayyaci Zakari da maman shi, Jummai Galadima zuwa ga gidan gwamnatin jihar Borno. Ya nuna yanda yake tsananin takama da hazakar yaron.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel