Inda ranka zaka sha kallo: Wutar lantarki ta kama wani barawo a garin Kaduna
Wani barawo mai mtsakaicin shekaru ya gamu da ajalinsa a lokacin da ya shiga cikin Turansfoma don kwashe wayoyin dake baiwa unguwar Yalwa dake yankin Talabishon na jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani mauzanin yankin mai suna Simon Dogo yana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na daren Asabar, 4 ga watan Agusta, inda yace:
KU KARANTA: Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ya roki Birtaniya ta dukunkuno Buhari zuwa Najeriya
“Ya samu nasarar yanke wata babbar wayar dake cikin Turansufomar, sai dai a lokacin da yake kokarin yanke waya ta biyu ne wutar ta ja shi, inda nan take ya mutu ba ko shurawa.” Don ko da majiyarmu ta kai ziyara yankin, ta tarar da gawan barawon kwance cikin jini.
Shugaban sashin watsa labaru na kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kaduna, KAEDCO, Abdula Azeez Abdullahi ya bayyana bacin ransa game da samun karuwar ayyukan barayin Turansufoma, inda yayi kira ga jama’a dasu sa ido.
Abdullahi yace a tsakanin wata daya an lalata tashoshin wutar lantarki guda goma a unguwar Barnawa kadai, inda yace hukumar ta lura akwai wasu gungun barayi da suka addabi na’urorin wutar lantarkin a kudancin Kaduna.
“Muna kira ga jama’a dasu kara sanya idanu akan na’urorin wutar lantarkin dake kudancin yankin Kaduna, domin mun samu rahoton wasu gungun barayi da suka fitini unguwannin Barnawa, Narayi, Sabon tasha, Television da Kachi.” Inji Abdullahi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng