Ta leko ta koma: An fasa bawa Najeriya bashin da zata gina titin jirgin kasa

Ta leko ta koma: An fasa bawa Najeriya bashin da zata gina titin jirgin kasa

- Burin ministan sufuri ya gamu da tasgaro

- Sakamakon matsalar da yarjejeniyar da aka cimma tazo da ita

- Amma duk da haka ministan ya ce zasu yi duk mai yiwuwa don cigaba da farfado da harkakokin sufurin jirgin kasa a kasar nan

Mininstan Sufuri na kasa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa matsalar kudi ce ta kawo tsaiko akan aikin ginin titin jirgin kasa wanda ya taso daga Ibadan zuwa Kaduna, duk da cewa akwai yarjejeniya da aka rattaba.

Rashin kudi ne ya haifar da tsaikon fara titin jirgin kasan zuwa Ibadan – Kaduna - Minista
Rashin kudi ne ya haifar da tsaikon fara titin jirgin kasan zuwa Ibadan – Kaduna - Minista

Amaechi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Warri, ya ce aikin za ayi shi ne da bashin da aka karbo daga bankin Exim da ke China, amma kawo yanzu kudin bai zo ba, wanda hakan ya kawo tsaiko fara aikin.

“Mun sanya hannu a yarjejeniyar da za ta ba mu damar karbo rancen kudi kimanin sama da Dalar Amurka biliyan $6.7billion, wanda hakan zai bamu damar fara aikin gina titin jirgin kasan cikin kwanciyar hankali, Amma Bankin da zai bada wannan makudan kudaden wato Bankin Exim da ke kasar China, ya bukaci mu rage yawan kudaden" in ji Amaechi

KU KARANTA: Zafafan tambayoyin EFCC sun sanya Mataimakin Saraki fara rashin lafiya

Ya kara da cewa gwamnatinsu ta yi nasarar samar da kudin da aka yi titin dogo wanda ya tashi daga Itakpe zuwa Warri tare kuma da kammala aikin titin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya lashe zunzurutun kudi kimanin $1billion.

A karshe ya bayyana cewa kimanin mutane 150 aka dauka aiki bayan kammala aikin titin dogo wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ya kuma ce wannan ba komai bane domin kuwa da zarar an kammala sauran layukan dogno, to babu shakka al'ummar kasar nan za su samu karin aikin yi.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng