Ba kada Ganduje ne a gabanmu ni da Kwankwaso ba – Shekarau

Ba kada Ganduje ne a gabanmu ni da Kwankwaso ba – Shekarau

A wata ganawa da manema labarai suka yi da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau yace ba kada gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne a gabansu ba shida Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba

Ganduje ba damuwa ne a gare mu ba ni da Kwankwaso - Inji Shekarau

Ganduje ba damuwa ne a gare mu ba ni da Kwankwaso - Inji Shekarau

A wata ganawa da manema labarai suka yi da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau yace ba kada gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne a gabansu ba shida Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

A bayanin da ya yiwa manema labarai ya ce, "Wannan abu daya faru mu tagomashi ne a gare mu. Domin duk wani dan siyasa na kirki, yana son karin koda mutum daya ne. Wannan ya zame mana alheri ga jam'iyyar PDP, ina maraba dashi kuma ina murna. Kamar yanda na taba fada a baya, ba shigowar Kwankwaso APC ce ta fitar damu ba, amma shigowar tasa ta iya zama kamar sanadi ga wadanda suka yi laifi, kuma suka yi rashin adalci sune shugabannin jam'iyyar APC na wannan lokacin, wanda a yanzu abinda jam'iyyar PDP ta ke yi kenan."

DUBA WANNAN: Saudiyya ta baiwa wani kamfani damar gina gidajen Sinima guda 30 a fadin kasar

Za ku amince da kungiyar Kwankwasiyya a cikin jam'iyyar PDP?

"To ni abinda na sani dai shine jam'iyyar PDP, kuma duk wanda yake da katin jam'iyya dan PDP ne. Saboda haka mai girma Rabi'u Musa Kwankwaso yana da iko ya zama yana da kungiya, kowacce iri ce doka bata hana shi ba. Illa dai tilas ne a san matakin jam'iyya daban, sannan matakin kungiya daban."

Ganin yanda kuka ringa adawa a baya, anya kuwa zaku iya zama jam'iyya daya da Kwankwaso?

"Babu abinda zai hana domin abubuwa ne na rayuwa, kuma ina ganin daga ni har shi munyi girman da zancen irin haka ma bai taso ba. Kuma ni a wurina wannan maganar ta wuce, kamar yanda na san shima ta wuce a wurin sa, mu yanzu babban abinda ke gaban mu daga ni har shi shine masalahar al'ummar mu da muke tafe tare dasu."

Amma hadin guiwar taku na nufin kuna son kwace gwamnati daga hannun Ganduje ne a Kano?

"A tsarina na siyasa, babu zancen mu hada kai domin mu cutar da wani ko a kori wani, zamu hada kai mu yi aiki a jam'iyyar mu domin jam'iyyar mu ta kai ga nasara a dukkanin matakan zabe. Amma babu zancen mu zo mu hadu don mu kada wani."

Akwai rade-radin cewa mutanenka suna tattaunawa da gwamnatin Kano domin komawa jam'iyyar APC.

"To nima duk naji wadannan rade-radi, a takaice wannan magana babu ita, ban yi ta da wani ba, ban kuma aika wani yayi ta da yawuna ba. Tunda ni dai nayi imanin babu wani tsohon Kwamishina, ko tsohon mai bani shawara da yayi min aiki da muka taba wannan zance dashi."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel