PDP zata kawo jihohin arewa 10 a 2019 – Sanata Danbaba

PDP zata kawo jihohin arewa 10 a 2019 – Sanata Danbaba

Sanata mai wakiltan mazabar Sokoto ta Kudu, Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba yace jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zata yi nasara a jihohin arewa 10 a zabe mai zuwa.

Danbaba na daga cikin yan majalisar da suka sauya sheka zuwa PDP a majalisar dokoki a kwanan nan.

Da yake jawabi ga wasu manema labarai a Sokoto a ranar Lahadi, yace bai yi danasanin barin jam’iyyar da ta sa ya zama Sanata ba saboda ba’a tafiya da su a lamuranta.

Ya ci gaba da bayanin cewa ya bar jam’iyyar saboda rashin daidaito, da rashin adalci ga dukkan mambobin jam’iyyar.

PDP zata kawo jihohin arewa 10 a 2019 – Sanata Danbaba
PDP zata kawo jihohin arewa 10 a 2019 – Sanata Danbaba

Danbaba wadda ya kasance mataiakin shugaban kwamitin sojoji na majlisa, yayi korafin cewa APC ta gaza magance manyan matsaloli uku na tsaro, tattalin arziki da cin hanci da rashawa wadda saboda su ne saka zabe ta a 2015.

Ya bayyana cewa mutanen dake kewaye da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke kai shi ga hanya mara bullewa sobada son zuciyarsu.

KU KARANTA KUMA: Abun dariya ne APC bata so Dogara ya bar jam’iyyar – Yan majalisar wakilai

Ya ce yana da Karin gwiwar cewa PDP zata yi nasa a jihohin Benue, Kaduna, Kano, Plateau, Kogi, Kwara, Bauchi, Gombe, Adamawa da Sokoto a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng