Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabon addinin 'yan hakika

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabon addinin 'yan hakika

Yayin kasar Najeriya ke cigaba da murmurewa daga bala'in da 'yan kungiyar ta'addancin Boko Haram dake ikirarin cewa su musulmai ne, kwatsam sai kuma ga wasu sun bulla su kuma da ke kiran kan su 'yan hakika.

Su dai wadannan mutanen da a halin yanzu suka fara daukar hankalin al'umma sun bayyana cewa su musulmai ne masu bin tafarkin darikar tijjaniyya duk kuwa da cewa malamai da jagororin ta sun nesanta kan su da ita.

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabon addinin 'yan hakika
Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabon addinin 'yan hakika

KU KARANTA: Mutane 5 da suka hana ni ficewa daga APC - Shehu Sani

Legit.ng ta samu cewa yan hakikar dai sun bullane a yankin arewacin Najeriya kuma yanzu haka suna ta kara samun mabiya musamman ma a tsakanin matasa.

Ga dai wasu daga cikin muhimman bayanai game da addinin da muka zakulo maku:

1. An ce dai yanzu haka hedikwatar su na a garin Ngurore da ke karamar hukumar Yola ta jihar Adamawa.

2. Ance haka zalika akwai birbishin su a jihar Nasarawa dake makwaftaka da babban birnin tarayya Abuja.

3. Mafi yawan ma su wannan akidar dai a boye suke yi ba a kasafai suke fitowa fili da ita ba.

4. Sukan bar yin sallah da Azumi.

5. Sukan yi musayar kwanciya da matan junan su na aure.

6. Mabiya akidar hakikar suna da ra`ayin cewa ba kowa ne zai fahimci koyarwar akidar ba sai wanda yake cikin kungiyar.

7. Galibinsu matasa ne, wadanda ba su wuce shekara 15-30 ba.

8. Mazajensu suna tara suma a kai, sannan suna rike katon carbi da suke nadewa a hannunsu.

9. Suna cudanya mazan su da mata.

10. Suna ikirarin cewa su `yan Tijjaniya ne, wadanda ke bin Sheikh Ibrahim Inyas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng