An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka

An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka

A yau Juma'a, Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da wasu manyan sauye-sauye da tayi wa manyan kwamandojin ta da ma wasu ma'aikatan.

Sabbin canjin da akayi ya shafi Kwamandan Operation Lafiya Dole dake Arewa maso Gabashin Najeriya da Kwamandan Jami'an tsaron hadin gwiwa (JTF).

Jami'an da aka yiwa sabbin naddin za su kama aiki ne a ranar 1 ga watan Augustan wannan shekarar.

A sanarwar da ta fito daga hannun Direktan Hulda da Jama'a na Sojin, Brig. Janar Texas Chukwuma, ya yi bayanin cewa an dauki matakin ne don kawo sabbin hannu cikin Operation Lafiya Dole don cinma burin Shugaban Sojin Najeriya, Lafatant Tukur Yusuf Buratai.

An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka
An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka

Sai dai wata majiya daga Hukumar Sojin tace shaidawa Daily Trust cewa canjin ba zai rasa nasaba da kissar da 'yan ta'adda da bata gari ke yiwa sojoji a wasu sassan kasar nan.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsige wani basarake a dan gatan gwamnan jihar Adamawa

Wadanda aka yiwa naddin sun hada da; Manjo Janar AM Dikko wanda zai kama aiki a matsayin Kwamandan Operation Lafiya Dole, sai Brig. Janar AO Abdullahi da zai fara aiki a matsayin Kwamandan Sector 2 na Operation Lafiya Dole sai Brig. Janar UU Bassey a matsayin Kwamandan Sector 3 na Operation Lafiya Dole.

Saura sun hada da Manjo Janar CO Ude a matsayin Kwamandan JTF Ndjamena, sai Manjo Janar J Sarham a matsayin Babban kwamandan 6 Division da kuma Manjo Janar EB Kabuk a matsayin Babban Kwamandan 82 Division.

Manjo Janar MS Yusuf shi kuma zai kama aiki a matsayin Babban Kwamandan 81 Division da Manjo Janar BA Akinroluyo a matsayin Kwamandan 3 Division.

Sanarwan kuma tace cikin manyan jami'an Sojin da canjin ya shafa sun hada da Manjo Janar Leo Irabor wanda zai kama aiki a matsayin Shugaban horaswa da ayyuka a Hedkwatan tsaro yayin da Manjo Janar LO Adeosun zai fara aiki a matsayin Shugaban horaswa da ayyuka a Hedkwatan Sojin Kasa.

Sauran da sauyin ya shafa sun hada da Manjo Janar JE Jakko da Manjo Janar AB Abubakar da Manjo Janar A Mohammed da Manjo Janar LKJ Ogunewe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164