Shugaba Buhari na ganawa da Sarakunan Gargajiya na Isoko a Fadar sa ta Aso Villa
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana mun samu rahoton cewa, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, na ganawa da Sarakunan gargajiya na Isoko a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.
An fara gudanar da wannan ganawa a dakin taro na Council Chamber dake fadar shugaban kasa da misalin karfe 12.00 na ranar yau ta Juma'a.
Shugabannin wannan yankin na Isoko dake jihar Delta sun roki shugaba Buhari kan tsawaita shirin nan na Amnesty Programme ga matasan su tare da sanya su cikin sahun nade-naden mukamai na gwamnatin tarayya.
Sun kuma yi kira ga shugaba Buhari akan ya kyutatawa al'ummar Isoko sakamakon zaman lafiya da kwanciyar hankali da suka tabbatar a yankin su na fiye da shekaru 15 tare da bayar da kariya ga kadarori da dukiyoyin man fetur da kuma makamashin gas dake yanki.
KARANTA KUMA: Dalilin da ya hana ni ficewa daga jam'iyyar APC - Shehu Sani
Shugaban wanna kungiya ta Sarakunan gargajiya kuma kakakin ta, Mista Iduh Amadhe, ya yi kira ga shugaba Buhari kana sanya idanun lura da kuma bayar muhimmanci wajen malala aikace-aikace na ci gaba a yankin na Neja Delta.
Amadhe ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta yi watsi da al'umma da yankin su na Isoko wajen nade-naden mukamai da kuma rashin kawo ci gaba musamman a harkokin ilimi, cibiyoyin masana'antu da kuma muhimman gine-gine na more rayuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng