Yan sanda na jiran isowar Saraki ofishin IRT a Abuja kan fashin Offa

Yan sanda na jiran isowar Saraki ofishin IRT a Abuja kan fashin Offa

Rundunar yan sandan Najeriya na zuba idanu don ganin isowar shugaban majalisar dattawa ofishin tawagar kwararru na IRT dake Guzape, Abuja kan fashin Offa wanda aka aiwatar a ranar Alhamis, 5 ga watan Afrilu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ofishin IRT na cikin fargaba yayinda aka tura jami’an yan sanda da dama yankin domin jiran isowar shugaban majalisar dattawan.

Legit.ng ta rahoto cewa ba’a sani ba ko Sanata Saraki zai amsa gayyatar da akayi masa.

Yan sanda na jiran isowar Saraki ofishin IRT a Abuja kan fashin Offa

Yan sanda na jiran isowar Saraki ofishin IRT a Abuja kan fashin Offa

Idan za ku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ya bukaci shugaban majalisar dattawa Bukola saraki da ya kai kansa ofishin IRT a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

Gayyatan na da alaka da bincike da ake yi kan fashin Offa da aka yi a ranar Alhamis, 5 ga watan Afrilu wadda yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel