Rashin albashi: Malaman makaranta 1,000 sun yi barazanar rataye kansu ranar 26 ga watan Yuli

Rashin albashi: Malaman makaranta 1,000 sun yi barazanar rataye kansu ranar 26 ga watan Yuli

Fiye da malaman makaranta 1,000 ne suka yi barazanar cewar zasu kasha kansu ta hanyar rataya matukar ba a biya su albashinsu cikin kwanaki biyu masu zuwa ba.

Fusatattun malaman makarantar sun bayyana cewar tsawon shekaru 12 kenan da gwamnatin jihar Assam dake arewa maso gabashin kasar ta dakatar da biyan malaman makaranta 12,000 albashi.

Daga cikin adadin, malamai 3,000 sun yi ritaya, yayin da 91 kuma sun dade da kasha kansu.

Kimanin malaman makaranta 1,514 ne a jihar Assam ke ikirarin cewar mahukunta sun dakatar da biyansu albashi saboda wata matsala da ba laifinsu ba.

Rashin albashi: Malaman makaranta 1,000 sun yi barazanar rataye kansu ranar 26 ga watan Yuli

Malamin makaranta
Source: Depositphotos

Yanzu haka malaman tare da iyalansu sun yi barazanar hallaka kan su ta hanyar rataya a ranar 26 ga watan Yuli, nan da kwana uku, muddin ba a biya su albashinsu ba.

DUBA WANNAN: Batanci: Jami'an tsaro sun mamaye makarantar da dalibi ya zagi annabi

Tun a shekarar 2006 ne gwamnati ta dauki malaman aiki kafin daga baya a sanar da su cewar an dauke su ne ba bisa ka’ida ba,” kamar yadda, Basanta Neog, sakataren kungiyar malaman da ba a biya albashin ya sanar da kafar yada labarai a yau, Litinin.

Duk da an bayyana cewar daukansu aiki ya sabawa ka’ida, malaman su 12,000 sun cigaba da koyarwa a makarantun firamare dake fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel