Wani matashin Tela mai shekaru 19 ya aikata ma yar uwarsa danyen aiki a Borno

Wani matashin Tela mai shekaru 19 ya aikata ma yar uwarsa danyen aiki a Borno

Rundunar Yansandan jihar Borno ta sanatr da cafke wani matashin Tela mai shekaru 19 bayan ya halaka ya uwarsa mai shekaru 35, Ya’Amsa Umaru, wanda take dauke da tsohon ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Damian Chukwu ne ya bayyana haka aranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, inda yace matashin ya jibga ma yar uwar tasa tabarya ne a gidansu dake karamar hukumar Magumeri.

KU KARANTA: Kiran ruwa babu lema: Fusatattun matasa sun halaka dakarun Soji guda 3

Matashin mai suna Abba ya halaka Ya’Amsa ne bayan ta matsa masa akan lallai sai ya dinka ma mahaifinsu sabon kaya, kamar yadda kwamishinan ya bayyana, inda daga bisani kuma ya binneta a cikin wani daki.

Haka zalika, kwamishinan ya kara da cewa jami’am Yansandan jihar sun kama wani matashi mai shekaru 20, Hassan Garba da laifin kashe wasu mutane biyu Hussaini Alhassan da Naziru Haruna a karamar hukumar Biu na jihar Borno.

Rahotanni sun ruwaito Hassan Garba yace ya kashe Hussaini da Naziru ne saboda yana zarginsu da aikata zina, don haka ya zama wajibi a gareshi ya yanke musu hukuncin kisan da ya hau kansu

“A ranar 18 ga watan Mayu ne Hussai dauke da adda ya kai ma Alhassan da Haruna hari yayin da suke cikin barci, wanda hakan yayi sanadin mutuwarsu, inda yace yayi hakan ne domin yanke musu hukuncin da ya dace dasu, sakamakon mazinata ne su.” Inji kwamishina.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel