'Yan bindiga cikin kayan jami'an 'yan sanda (SARS) sun budewa motar Dino Melaye wuta
- Wasu 'yan bindiga sanye da kakin 'yan sanda sun budewa ayarin motocin Sanata Dino Melaye wuta
- Labarin ya haifar da firgici a tsakanin al'ummar yankin da abin ya faru
- Wasu kangararrun matasa sun kone wasu ajuzuwan makaranta da Dino Melaye ya gina a wasu mazabu
Rahotanni dake iske mu a wannan lokaci, sun tabbatar da mana cewar wasu 'yan bindiga sanye da kakin jami'an 'yan sanda na SARS sun budewa tawagar Sanata Dino Melaye wuta a jihar Kogi.
Jaridar Tribune ta rawaito cewar lamarin ya faru ne a yankin Ayetero-Gbede dake karamar hukumar Ijumu inda Sanata Melaye ya je bude wasu aiyuka.
Jaridar ta bayyana cewar 'yan bindigar dake ciki wasu motoci 6 samfurin Hilux sun datse hanyar Dino Melaye daga garin Mopamuro zuwa Ayetoro kuma tawagar Sanatan na kawo kai suka bude mata wuta.
DUBA WANNAN: 2019:Tinubu na fuskantar matsin lamaba daga na hannunn damansa a kan goyon bayan takarar Buhari
Mai taimakawa Sanata Melaye a bangaren yada labarai, Gideon Ayodele, ya ce jami'an tsaro ne suka kaiwa Sanatan harin.
A kwanakin baya ne wasu matasa da ba a san ko su waye ba suka kone wasu ajuzuwan da Sanata Melaye ya gina a wata makarantar sakandire ta mata dake mazabar Sarkin Noma da Lokon Gama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng