Wani dan sanda ya kashe dan acaba saboda ya hana shi cin hancin naira 100
- An kashe wani dan acaba a jihar Delta
- An kashe shi saboda ya hana dan sanda cin hancin naira 100
- Matasa sun kusa kone ofishin 'yan sanda
A jiya ne wani dan sanda ya kashe wani dan acaba, saboda ya hana shi cin hancin naira 100, akan hanyar Issele - Uku/Issele - Mkpitime dake Asaba a jihar Delta.
Wasu shaidu sun bayyana cewar, 'yan sandan sun haushi da duka ne, inda suke tambayar shi ya basu naira 100, shi kuma yaki bayar wa, abinda ya fusata daya daga cikin su kenan, ya doka mishi gindin bindiga a kai, sanadiyyar mutuwar shi kenan.
DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP ta zargi fadar shugaban kasa da kokarin rufe cin hanci da rashawa
Abinda ya fusata 'yan acaba da matasa na yankin wurin, suka nufi ofishin 'yan sanda na Onicha - Olona da niyyar kone shi, sai dai hakan bai yiwu ba, saboda 'yan sanda masu kokarin kwantar da tarzoma sun zo wurin, suka hana su kone wurin.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Andrew Aniamaka, ya shaidawa majiyarmu Legit.ng a wayar tarho cewar basu ji dadi ba da matasan suka nemi daukar mataki da hannun su.
Ya kara da cewar har yanzu basu samu wani rahoto ba dake nuna cewar kisan ya faru.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng