Tufka da warwara: Ina nan daram dam a APC – Gwamnan Benue, Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce yana nan daram-dam a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, 19 ga watan Yuli a sakatariyar jam’iyyar APC bayan ganawar sirrin da yayi da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.
A farkon makon nan, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnan ya bayyana cewa an bashi jan kati kuma saboda haka ya bar jam’iyyar. Daga baya ya bayyana cewa ya fadi hakan ne saboda rikicinsa da tsohon gwamnan jihar, Sanata George Akume.
Bugu da kari, a ranan Laraba ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP da kuma yan kungiyar R-APC a Ilori, jihar Kwara.
KU KARANTA: Osinbajo, gwamnoni, shugaban NNPC, gwamnan CBN, sun shiga ganawar gaggawa
A yau kuma, ya canza maganarsa inda yace: “Wani sanata a jihar Benue wanda yake shugabansu ya bani jan kati kuma na dauki abin da gaske.”
“Amma shugabancin jam’iyyar sun fada min cewa matsayar shugabannin jam’iyyar yafi na kowani ma’aluki kuma haka ya gamsar da ni.”
“Mun yi magana da shi (Oshiomole), za’a magana da masu ruwa da tsaki kuma nan ne matsayata. Bamu kammala maganar ba, an kan yi.”
“Ina nan a jam’iyyar APC, ni mamban APC ne, har ila yau inda daga tutan APC, abinda nace kawai shine an bani jan kati kuma shugabancin jam’iyyar sun min gyara a kan hakan.”
Yayinda yake nune godiyarsa ga jam’iyyar, ya ce yana kyautata zaton shugabannin za su shawo kan al’amarin.
Asali: Legit.ng