Al’umma a jihar Kano sun yi barazanar kauracewa zaben 2019
- Al’ummar wasu yankunan jihar Kano sun yi barazanar kauracewar zaben shekarar 2019 saboda lalacewar hanyoyinsu
- Kazalika sun yi barazanar kauracewa allurer rigakafi ta Polio muddin gwamnati bata gyara masu hanyoyinsu ba
- Mazauna yankunan na fama da rashin kyan hanyoyi da zaizzayar kasa da suka saka su cikin hatsarin ambaliyar ruwa
Mazauna wasu unguwanni 5 dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano sun yi barazanar kauracewa zaben shekarar 2019 da kuma allurar rigakafin Polio muddin gwamnati bata gyara masu hanyoyinsu ba.
Unguwannin da suka yi wannan ikirarin su ne; Na’ibawa ‘Yan lemo, ‘Yan Tasi, Mai Kalwa, Wailari, Kwarin Goje da Umarawa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rahotannin sun bayyana cewar mazauna unguwannin na fama da lalacewar hanya, zaizayar kasa da kuma ambaliyar ruwa saboda rashin magudanan ruwa.
Alhaji Nura Danjuma, shugaban gamayyar kungiyoyin unguwannin, ya bayyana cewar sun sha mika kukansu ga mahukunta a jihar amma har yanzu ba a yi komai a kai ba.
DUBA WANNAN: 'Yan sandan tawagar Osinbajo sun zane jami'an Kwastam a Katsina
Yayin da wakilin jaridar Daily Trust ya kai ziyara unguwannin, ya ga yadda zaizayar kasa ta cinye fiye da rabin hanyoyin da suka shiga da kuma fita unguwanni daga cikin gari.
Danjuma ya bayyana cewar sun yanke shawarar kin fitowa domin kada kuri’a a zaben 2019 ne domin nunawa gwamnati fushinsu tare da jaddada cewar babu gudu, babu ja da baya matukar ba a saurari kukansu ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng