Tsare-tsarenka na iya kawo sauyi a Najeriya – IBB ga Turaki
Dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin lemar jam’iyyar PDP, Barista Kabiru Tanimu Turaki (SAN) ya ziyarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida domin neman goyon bayansa a kudirinsa na son takara.
Tsohon shugaban kasar ya nuna gamsuwa da manufofin Turaki inda ya jadadda cewa wannan tsare-tsare na shi na iya sauya lamuran kasar.
Dan takarar na PDP da yake gabatar da tsare-tsaren day a tanadarwa kasar ya ce sun hada da magance rashin tsaro, habbaka tattalin arziki tare da kara yawan matasa da za’a dauka aiki.
Tsohon shugaban kasar yace babu shakka idan aka ba Turaki damar shugabancin kasar zai tabuka abun kirki domin tanadin da yayiwa kasar.
KU KARANTA KUMA: Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi
Ya kuma goyi bayan kira da dan takarar yayi kan cewa ya kamata a riki lamarin hada kan Najeriya fiye da dukkanin lamura, cewa ba’a taba samun rabuwar kai hakan ba cewa “akwai bukatar a kara hada kanmu kuma manufarka zai iya aiwatar da hakan.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng