Har ila yau: Wata gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar garin Kano
A kalla shagun shida ne suka gobara ta lashe a kasuwar Kofar Wambai da aka fi sani da Kauwar 'Yan Yeri a daren jiya Juma'a.
Direktan Hukumar Kiyaye Gobara ta jihar, Sagir Madaki, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa gobarar ta kone shaguna guda shida a yau Asabar a Kano.
Madaki yace sun samu koke daga ofishin Yan sanda na Kofar Wambai misalin karfe 8.57 na dare cewa gobara ta barke a kasuwar ta Wambai.
DUBA WANNAN: EFCC ta karyata zargin Magu da cinye kudin alawus din ma'aikata
"Da samun sakon, munyi hanzari mun aike da wasu ma'aikatan mu tare da motoccin kashe gobara zuwa kasuwar, sun kwashe misalin mintuna 55 kafin su kayi nasarar kashe wutan saboda kar ta bazu zuwa wasu shaguna." Inji Madaki
Direktan hukumar kashe gobarar yace har yanzu ana gudanar da bincike don gano musababbin afkuwar gobarar.
Ya shawarci yan kasuwa da sauran mutane su kiyaye wajen amfani da na'urori da ka iya tayar da wuta saboda kiyaye afkuwar abu mai kama da wannan a gaba.
Har ila yau, Direktan ya kuma shawarci mutane su rika ajiye bokitin kashe wuta, da bargon kashe wuta har ma da na'urar kashe gobara 'Fire Extinguisher' domin hakan zai taimaka musu wajen tsagaita wutar kafin jami'an kashe gobarar su iso.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng