Ina zawarawa da 'yan mata, Dangote yace yana bukatar sake kara mata
Hamshakin dan kasuwa da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya sanar da cewa yana neman matar aure.
Attajirin mai shekaru 61 a duniya ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da David Piling na Financial Times. Ya kuma bayyana cewa ya yi aure a baya har sau biyu amma sun rabu da matansa saboda yanayin aikinsa.
"Girma na karuwa, shekaru 60 ba wasa bane amma bai dace mutum ya yi aure ba idan ya san bashi da lokacin iyalinsa. A halin yanzu akwai ayyuka sosai a gabanmu kamar gina matatan man fetur da kamfanin takin zamani da kuma ginin bututun iskar gas."
Sai dai ya amince da cewa lokaci ya yi da ya kamata ya 'dan huta.
DUBA WANNAN: Da Azikiwe yana raye tabbas zai goyawa Buhari baya
Dangote ya kuma bayyana wasu abubuwan ban mamaki shida da mutane basu sani game dashi ba
1) Yana Azumi a kalla sau daya a duk mako
Duk da irin kamfanoni da masan'antu da attajirin ya mallaka, ya fadawa Pilings cewa yana kokarin yin azumi a kalla sau daya a mako saboda azumi na karfafa garkuwar jiki.
2) Yana amsa waya sama da 100 a duk rana
Kamar yadda aka sani, ba abin mamaki bane mutumin da yafi arziki a Afirka ya kasance yana samun sakoni da kirar waya da yawa.
A lokacin da yake magana kan dangantakarsa da tsohon Firai Ministan Ingila, Tony Blair, Damgote yace waya uku katchal Blair ke amsawa a rana amma shi yana amsa sama da 100.
3) Yana zon ganin Najeriya ta zama kasar da tafi kowace fitar da albarkatun man fetur a Afirka
Attajirin ya bayyana cewa da zarar an kammala matatan man fetur dinsa, Najeriya zata zama kasar da tafi kowace samar da albarkatun man fetur a Afirka.
4) Yana son Najeriya ta dena siyo madara daga kasashen waje
Dangote yace yana takaicin yadda Najeriya bata iya ciyar da kanta hakan yasa yake so a tsaurara doka kan shigo da abincin kasashen waje.
"Najeriya tana shigo da 97 zuwa 98% na madarar da muka amfani dashi. Ya kamata gwamnati ta kafa dokar hana shigo da madara kamar yadda akayi wa Siminti."
5) Har yanzu yana kan bakansa na son siyar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal
Ina matukar son Arsenal kuma har yanzu ina kan baka ta na siyan kungiyar.
Dangote yace muddin ya kammala gina matatan man fetur dinsa, zai mayar da hankali kan batun siyan Arsenal. Ya kiyasta kuddin kungiyar zata kai $2 biliyan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng