Daga karshe: Lauya musulma tayi nasara a kan makarantar horon lauyoyi, an yaye ta da hijabinta

Daga karshe: Lauya musulma tayi nasara a kan makarantar horon lauyoyi, an yaye ta da hijabinta

A yau ne makarantar horon lauyoyi ta kasa dake jihar Legas ta yaye lauyar nan musulma, Barista Amasa Firdausi, bayan an ki yaye ta a baya saboda ta ki cire hijabinta yayin da ake yaye ragowar abokan karatunta.

A watannin baya ne kafafen yada labarai suka watsa rahoton yadda makarantar horon lauyoyi ta ki yaye Firdausi saboda ba ta cika ka’idar saka sutura ta karatun lauya ba.

Firdausi ta je wurin yaye lauyoyin bayan kammala karatunsu sanye da hijabi, lamarin da ya saka mahukunta a makarantar umartar ta da ta canja shigar ta zuwa ta ragowar abokan karatunta amma sai taki amincewa da hakan tare da bayyana cewar ba zata canja salon shigarta da addininta ya amince ta yi ba.

Daga karshe: Lauya musulma tayi nasara a kan makarantar horon lauyoyi, an yaye ta da hijabinta

Lauya Fiddausi yayin yaye ta

Takaddama a kan batun saka hijabin ya jawo barkewar cece-kuce a Najeriya. A yayin da wasu ke ganin laifin mahunkuntar makarantar, wasu kuwa sun bawa Firdausi laifi ne musamman ganin cewar tun farko ba karatun addini ne ya kai ta wurin ba.

DUBA WANNAN: ‘Yan sanda sun haramta duk wani taron jama’a gabanin gurfanar da El-Zakzaky gobe

Kazalika wasu manyan lauyoyin kasar nan sun tafka mahawara a kan batun kin cire hijabin da Firdausi ta yi. Wasu daga cikin manyan lauyoyin sun bayyana cewar babu alaka tsakanin yanayin shigar mutum da kuma bas hi sakamakon ko shaidar zama lauya muddin ya yi nasara a dukkan jarrabawa da ya rubuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel