Wata Baiwar Allah da ke daf da kammala Jami’a ta rasu a gidan wani Saurayi

Wata Baiwar Allah da ke daf da kammala Jami’a ta rasu a gidan wani Saurayi

Labari ya kai gare mu cewa wata Baiwar Allah mai suna Adenike Olubayo wanda ‘Diya ce wurin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Lasisi Olubayo ta rasu a Ranar Lahadin nan da ta wuce.

Adenike Oluboyo wanda Mahaifin ta ne ya sauka daga kan kujerar Mataimakin Gwamna na Jihar Ondo a wancan Gwamnatin na baya ta cika ne a Garin Akure a dakin wani Saurayin ta mai suna Adeyami Alao wanda aka fi sani da QS.

Wata Baiwar Allah da ke daf da kammala Jami’a ta rasu a gidan wani Saurayi
Adenike Oluboyo ta rasu yayin da ta ke shirin gama karatu

Kamar yadda Jami’an ‘Yan Sandan Yankin su ka tabbatarwa manema labarai NAN, an tsinci gawar yarinyar ne da safe. Femi Joseph wanda shi ne ke magana da bakin ‘Yan Sandan Jihar Ondo ya fadawa ‘Yan Jarida wannan labari.

KU KARANTA: An nemi Shugaba Buhari ya biya Abiola hakkokin sa

Kafin rasuwar wannan Baiwar Allah dai ta na karatu ne a Jami’ar Adekunle Ajasin inda ta ke gaf da kammala makaranta. Hukumar ‘Yan Sanda tace tana bincike game da lamarin kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda zai yi jawabi da kan sa.

Mu na jin kishin-kishin din cewa an ga gawar Marigayiya Adenike Oluboyo ne a karkashin gadon saurayin na ta wanda aka fi sani da Q.S. Ana dai sa rai ba da dadewa ba Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar yayi wa Jama’a cikakken bayanin halin da ake ciki.

Jiya kun samu labari cewa wasu Mabiya addinin Musulunci da ba a san da irin su ba sun shigo cikin Kasar nan inda su ke daukar Mabiya musamman a cikin Arewacin kasar a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng